Kasuwanci

DALILIN MAWAKIYA RIHANA KAMFANIN SNAPCHAT A SARAR DALA BILYAN DAYA

Tsokanar shahararriyar mawakiyar Amurka, Rihanna da Snapchat ya yi, ta haifar wa kamfanin asarar dalar Amurka biliyan daya.

A ‘yan kwanakin nan ne kamfanin Snapchat ya yi wata talla mai taken “Ku sharara wa Rihanna Mari”.

Abinda yasa nan take mawakiyar ta mayar da martani a fusace inda ta tura wa masoyanta goron gayyata da su juya wa kamfanin baya.

Janyewa daga shafin shafin zada zumunta na Snapchat da milyoyin magoya bayan Rihanna suka yi, ya haifar wa kamfanin da asarar zunzurutun kudi dalar Amurka biliyan daya a kasuwar hannayen jari ta duniya.

Tallar da Snapchat ya yi,na yin tuni ne kan wulakancin da mawakiyar ta yi fama da shi a shekarar 2009, a hannun tsohon mijinta dan gambara Chris Brown.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *