Addinai Labarai

Malamai Sun Magantu Kan Batun Auren Fatima Ganduje Daga Aminu Bashir Medile

Malamai Sun Magantu Kan Batun Auren Fatima Ganduje

Daga Aminu Bashir Medile

Malaman addini da dama a Nigeria sun yi magana dangane da abinda ya faru a yayin shagalin auren ‘yar mai girman gwamnan Kano wanda aka yi a makon da ya gabata, ga dai wasu daga maganganun maluman:-

1. “Shi addinin musulunci Allah cewa yayi “ KU SHIGA MUSULUNCI DARI BISA DARI” kamar yanda zamuyi sallah a masallaci haka zamuyi kasuwanci yazamo akwai addini tsantsa a ciki. Haka zamuyi walima da bikinmu da tsoron Allah batare da bayyana wani abu da yake na sabon Allah ba. Dukkanin rauwar mu haka mata aga alama ta musulunci da tsoron Allah, muna kira ga shugabanni suji tsoron Allah dangane da amanar da Allah ya dora musu Annabi yace “shugaba mai kiwo ne a cikin al’ummarsa kuma Allah zai tambayeshi gameda kiwon daya bashi” shine ya dorasu zuwa ga hanya ta tsoron Allah, hanya ta da’a , hanya ta taqawa hanya ta kamun kai hanya ta kunya hanya ta kamewa hanya ta nuna mutunci da nuna kamala cikin al’adunmu masu kyau na hausawa al’adunmu na musulunci da muka gada a musulunci. Su yakamata mununawa wasu mutane, amma kwaikwayo da muke na wasu dabi’u banamu ba wannan aibune garemu”. -Sheikh Ali Yunus Limamin masallachin UthamnaUthman bn affan dake Kano.

2. “Zancen fasiqancin da ake hanawa. Komai kirkin ka bani adam kaga mace an rungumeta a titi kaima bani adam yaza kaji komai tsoron Allanka sai sha’awa ta kamaka abinda akeyinsa a daki azo ana yinsa a internet, ya za’a zauna lafiya, abune a boye ake yinsa azo ana yinsa a bayyane”. -Sheikh Abdukwahab Abdallah

3. “Talaka yanayin fajirci amma tasirin barnar talaka bata giriza al’umma irin tasirin barnar me fada aji barnar shugaba basarake ko attajiri ko malamin addini ya ‘yan uwa Allah subhanahu wata’ala ya koyarda mu yadda zamu gode masa in yaimana ni’ima ko waccece kuwa domin ba daga kanmu aka faraba idan shugabane ya aurar da yarsa talakane ya aurar da yarsa attajiri ne ya aurar da yarsa manzon Allah ya koyamana irin yadda akeyin walima a godewa Allah a ci a sha. Anas dan malik yake cewa lokacin da manzon Allah (s.w.a) ya auri nana Zainab shi ya turani naje na kirawo mutane suzo walima , mutane su kaci sukasha.
Manzon Allah yaje walimar aure a madina ango da amaryar su suke raba abinci a wajen, amman amaryar bata fito tsirara ba ba tayi rawa ba batayi rashin kunya ba. Manzon Allah yana zaune yana cin abinci dashi da sauran sahabansa.
Don haka bamuda bukatar dauko wasu dabi’un wasu marasa kyau wanda suke cin karo da addinin mu wanda kuma zasu yada barna da fasadi a cikin al’ummar mu”. Sheikh Lawan Abubakar Shu’aib limamin masallacin Triumph dake Kano.

4. Kunga yadda Allah ya maida dumush, kunga yanda Allah ya maida garuruka Allah ya halaka su. Wallahi kano idan basuyi hankali ba Allah zai halakasu. idan basuyi hankali ba sun zabi mutanan da suke tsoron Allah ba. Tsoron Allah da wannan fasikanci Allah zai iya halaka garin kano, kunga”. -Dr. Ahmad Gumi.

Allah ya kyauta.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *